Majalisar dinkin duniya da kasar Japan ne suka bukaci kwamitin mai kunshe da mambobi 15 da ya gudanar da taron a safiyar yau laraba.
Tuni dai Amurka ta caccaki Korea ta Arewa yayinda ta bukace ta da ta mutunta dokokin kasa da kasa.
Gwamnatin Korea ta Arewa ta fito karara, inda ta sanar da yin gwajin duk da cewa hukumar hana yaduwar makamin Nukliya ta haramta haka.
Sanarwar da aka yi a kasar ta kafar talabijin, ta ce gwamnatin kasar ta samu gagarumar nasarar gwajin makamin a yau laraba, 6 ga watan Janairu da misalin karfe 10 na safe agogon kasar.
Kafin dai sanarwar, hukumar binciken girgizar kasa ta Amurka ta ce ta ji wani kara da ke kama da girgizar kasa a Korea.288